Jummaʼa 17 Afirilu 2026 - 14:09
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdiyya (16) | Sanya Lokacin Bayyanar Imam Mahdi (AJ)

Hauza/ Tun da daɗewa akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin ayyana lokacin bayyanar Imam Mahdi (AJ) saboda wasu mugayen dalilai, kuma irin waɗannan mutane za su ci gaba da bayyana a nan gaba. Saboda haka, Imamai Ahlul Bayt (AS) sun ja hankalin muminai kada su yi shiru a gaban masu ƙayyade lokacin bayyanar Imam, sai dai ma su ƙaryata su.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ana gabatar da wannan jerin tattaunawa mai take “Zuwa ga Al’umma Mai Manufa” da nufin yada ilimi da koyarwar da suka shafi Imam Mahdi (AJ) ga masu karatu.

Ɗaya daga cikin tambayoyin da ake yawan yi shi ne: Yaushe Imam Mahdi (AJ) zai bayyana? Shin an taɓa sa masa lokaci?

Amsar, bisa ga hadisai, ita ce: Lokacin zuhur  yana ɓoye ga mutane.

Dangane da haka Imam Sadiƙ (AS) ya ce:

«کَذَبَ اَلْمُوَقِّتُونَ مَا وَقَّتْنَا فِیمَا مَضَی وَ لاَ نُوَقِّتُ فِیمَا یَسْتَقْبِلُ.» (الغیبه، شیخ طوسی، ج ۱، ص ۴۲۶)

“Masu ƙayyade lokaci sun yin ƙarya. Mu ba mu taɓa ayyana lokaci a baya ba, kuma ba za mu ayyana shi nan gaba ba.” (Al‑Ghayba, Sheikh Tusi, j.1, sh. 426)

Don haka, duk wanda ya ayyana wani lokaci domin zuwan Imam Mahdi (AJ), maƙaryaci ne. Wannan maimaitaccen batu ne a cikin ruwayoyi.

Imam Baƙir (AS) ya ce wa ɗaya daga cikin sahabbansa da ya tambayi lokacin zuhur:

«کَذَبَ الوَقّاتونَ، کَذَبَ الوَقّاتونَ، کَذَبَ الوَقّاتونَ.» (الغیبه، شیخ طوسی، ج ۱، ص ۴۲۵)

“Masu ƙayyade lokaci sun yi ƙarya, sun yi ƙarya, sun yin ƙarya.” (Al‑Ghayba, Sheikh Tusi, j.1, sh. 425)

Daga waɗannan hadisai ana iya fahimtar cewa tun da daɗewa akwai mutane masu ayyana lokaci saboda son zuciya, sannan kuma za su ci gaba da bayyanawa a nan gaba. Saboda haka ake umurtar muminai da kada su yi shiru—su ƙaryata su.

Imam Sadiƙ (AS) a kan haka ya cewa wani sahabinsa:

«مَنْ وَقَّتَ لَکَ مِنَ اَلنَّاسِ شَیْئاً فَلاَ تَهَابَنَّ أَنْ تُکَذِّبَهُ فَلَسْنَا نُوَقِّتُ لِأَحَدٍ وَقْتاً.» (الغیبه، شیخ طوسی، ج ۱، ص ۴۲۶)

“Idan wani ya ayyana maka lokaci (na zuhur), kada ka ji tsoro ka ƙaryata shi, domin mu ba mu ayyana lokaci ga kowa ba.”

(Al‑Ghayba, Sheikh Tusi, j.1, sh. 426)

Wannan tattaunawar za ta ci gaba…

An ɗauko daga littafin “Negine Afarinesh” tare da ɗan gyara.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha